Isa ga babban shafi
Tunisia

Tunisia: An kashe mutumin da ake zargi ya kashe Chokri Belaid

Gwamnatin kasar Tunisia ta tabbatar da mutuwar Kamel Gadhgadhi, wanda ake zargi ya kashe jagoran adawa Chokri Belaid a wani samame da ‘Yan sanda suka kai kan ‘Yan ta’adda inda aka kashe mutane shida cikinsu har da dan sanda guda.

Lotfi Ben Jeddou, ministan cikin gida a Tunisia
Lotfi Ben Jeddou, ministan cikin gida a Tunisia REUTERS/Zoubeir Souissi
Talla

Wannan na zuwa ne duka saura kwanaki biyu a cika shekara guda da aka kashe Chokri Belaid.

Kisan Belaid ya janyo wa Jam’iyyar ‘Yan uwa Musulmi ta Ennahda baraka tare da sake hura wutar zanga-zangar kin jinin gwamnati a kasar Tunisia.

Belaid shi ne mutum na biyu daga bangaren adawa da ake zargin Mayakan Jihadi sun kashe a bara wanda hakan ya rusa gwamnatin Jam’iyyar Ennahda bayan fuskantar suka daga bangaren ‘yan adawa masu son kafa gwamnatin ‘Yan boko zalla.

Ministan cikin gida Lotfi Ben Jeddou yace a ranar Litinin ne jami’an tsaro suka kaddamar da samamen a wani gida da ke yankin Raoued a Tunis inda suka kashe ‘Yan bindiga guda bakwai kuma cikinsu akwai Kamel Gadhgadhi wanda ministan yace shi ne ya kashe Chokri Belaid.

Mahukuntan Tunisia sun ce akwai makamai da bindigogi da kudade da aka samu a cikin gidan da mayakan ke buya.

A ranar 6 ga watan Fabrairu ne aka kashe Chokri Belaid a harabar gidansa wanda shi ne sakatare Janar na Jam’iyyar adawa ta PPDU a Tunisia.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.