Jam’iyyar Essebsi ta yi ikirarin lashe zaben Tunisia
Beji Essebsi ya bayyana samun nasara a zaben shugaban kasa da aka gudanar a kasar Tunisia da yayin da shuagban kasa Moncef Marzouki ya yi watsi da ikrarin. Essebsi mai shekaru 88 ya yi jawabi gaban magoya bayansa 2,000 da suka hada gangami a Cibiyar Jam’iyar, yana mai bayyana godiya ga goyan bayan da suka ba shi.
Wallafawa ranar:
Marzouki wanda shi ne shugaban rikon kwarya yace ikirarin Essebsi ya sabawa dimukuradiya.
Wannan ne karon farko da aka gudanar da zaben shugaban kasa a Tunisia bayan kawo karshen mulkin Zine Al Abidine Ben Ali.
A yau Litinin ne ake saran hukumar zaben kasar za ta bayyana sakamakon zaben.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu