Isa ga babban shafi
CAN 2015

Tunisia da DRC sun kai kwata Fainal

Tunisia da Jamhuriyar Congo sun kai ga zagayen kwata Fainal bayan sun tashi ci kunnen doki ci 1 da 1 a karawar da suka yi a gasar cin kofin Afrika da ake gudanarwa a kasar Equatorial Guinea. Yanzu an yi waje da Zambia da Cape Verde wadanda suka tashi babu ci.

'Yan wasan Tunisia
'Yan wasan Tunisia Cafonline.com
Talla

A ranar Assabar ne Tunisia za ta hadu da Equatorial Guinea a zagaye na gaba, yayin da kuma Jamhuriyar Congo ta hadu da makwabciyarta Congo Brazzaville.

A yau ne kuma ‘yan rukunin C da ake kira na mutuwa za su fafata.

Algeria za ta kara ne da Senegal a Malabo, yayin da kuma Ghana ta fafata da Afrika ta kudu a Mongomo.

Dukkanin kasashen dai na iya tsallakewa, kuma maki guda ne Senegal ke nema, don haka kunnen doki ya isa ta tsallake zuwa zagaye na gaba.

Ghana da Algeria kuma dukkaninsu suna neman maki uku ne, yayin da kuma Afrika ta kudu ke neman nasara tare da fatar Senegal ta doke Algeria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.