Isa ga babban shafi
CAN 2015

Kamaru da Cote d’Ivoire sun tsira da maki guda

Kasashen Kamaru da Cote d’Ivoire sun samu tsira da maki guda a karawarsu ta farko a gasar cin kofin Nahiyar Afrika bayan sun yi kunnen doki a fatawarsu da Mali da kuma Guinea a rukuninsu na D.

Sambou Yatabare, dan wasan kasar Mali
Sambou Yatabare, dan wasan kasar Mali REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Core d’Ivoire ta yi kunnen doki ne da Guinea kuma Saydou ne ya kwaci Cote d’Ivoire wanda ya farke kwallon da Guinea ta fara jefa wa a raga bayan alkalin wasa ya ba Gervinho jan kati a wasan.

Haka kuma Kamaru ta yi kunnen doki ne da Mali, amma Kamaru ta sha da kyar ne domin Mali ce ta fara jefa kwallo a raga.

Sai a ranar Assabar ne kasashen a rukunin na D za su sake fafatawa a Malabo inda Cote d’Ivore za ta kara da Mali, kamaru kuma ta fafata da Guinea.

A yau Laraba kuma mai masaukin baki ce Equatorial Guinea za ta kece raini da Burkina Faso, yayin da kuma Congo Brazzaville ta fafata da Gabon.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.