Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka na ci gaba da kai hari a Iraqi

Amurka ta ci gaba da kai hare hare ta sama kan yankunan da ke hannun ‘yan tawayen Iraqi, tare da sako kayayyakin agaji ga jama’ar yankin. Wannan na zuwa ne a daidai loklacin da shugaba Barak Obama ya lashi takobin ceto dubun bubatar fararen hulan da mayakan suka yi wa kawanya.Rundunar sojan na Amurka ta bayar da sanarwar cewa sojojin sun sami nasarar kai hare hare har guda 4, don samar da kariya ga fararen hula ‘yan kabilar Yazidi, da suka tsere zuwa tsaunin Sinjar, sakamakon harin da mayakan na jamahuriyar Islama ke kaiwa a arewacin kasar.A halin da ake ciki kuma, ministan harkokin wajen Faransa Laurent Fabius na kan hanyar shi zuwa Iraqi, inda zai je biranen Arbil da Bagadaza, don tattaunawa da shugabannin kasar.Mr Fabius da ya bar birnin Parin yau Lahadi, zai fara ganawa da takwaranshi na Iraqi Hoshyar Zebari a birnin Bagadaza, kafin ya wuce zuwa Birnin Arbil, inda sojan Amurka suka kaddamar da hare hare kan mayaka masu kishin Islama a arewacin kasar.A birnin na Arbil ministan zai duba yadda ake kai kayan agaji ga fararen hulan yankin, da suka tsere wa rikicin. 

Wasu 'yan kabilar Yazidi da suka tsere daga gidajensu, sakamakon yakin kasar Iraqi
Wasu 'yan kabilar Yazidi da suka tsere daga gidajensu, sakamakon yakin kasar Iraqi Reuters
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.