Iraq
Mayakan IS sun kori Kiristocin Iraqi
‘Yan bindiga da ke gwagwarmayar shinfida daular musulunci a Iraqi sun karbe ikon garin Qaragosh mai yawan mabiya addinin Kirista tare da tursasawa daruruwan Kiristoci ficewa daga yankin. Wani Malamin Kirista ya shaidawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa Mayakan sun mamaye wuraren da Kiristoci ke ibada tare da tarwatsa kayan da suke ibada da kona littafan addininsu.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce Kiristoci sama da dubu dari sun kauracewa gidajensu.
Tun a watan Jiya ne Mayakan ISIS suka mamaye yankin arewaci Iraqi da wani yanki na Syria.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu