Isa ga babban shafi
Iraq

Mayakan Iraqi sun karbe ikon Sinjar

‘Yan bindiga da ke fada da gwamnatin Iraqi sun kafa tutarsu a garin Sinjar da suka kwace a kwanaki biyu da suka kwashe suna gwabza fada da Sojojin yankin Kurdistan mai cin gashin kai a Iraqi. Rahotanni sun ce Kurdawan da ke rayuwa a Sinjar sun fice bayan Mayakan da suka ayyana kafa daular Islama sun kwace garin.

Mayakan Iraqi da ke gwagwarmaya a garin Mosul
Mayakan Iraqi da ke gwagwarmaya a garin Mosul Reuters
Talla

Wani Jami’in gwamnatin Kurdawa ya shaidawa Kamfanin Dillacin labaran Faransa cewa ‘Yan bindigar sun ja Tutarsu sama baka mai dauke da sunan Allah a gine-ginen gwamnati.

Yanzu haka kuma daruruwan ‘Yan gudun hijira da suka fake a yankin Sinjar saboda rikicin Iraqi  ba su san makomarsu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.