Isa ga babban shafi
Iraqi-Amurka

Amurka za ta kaddamar da hare haren a Iraqi

Shugaban Amurka Barack Obama ya bayar da umurnin a kaddamar hare hare ta sama akan Mayakan IS da suka mamaye arewacin Iraqi da wani yanki na Syria. Obama yace za a yi amfani da jiragen yaki domin kai kayan abinci ga ‘yan gudun hijira.

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama REUTERS/Larry Downing
Talla

A cewar Obama, Amurka ta dauki matakin ne domin hana aukuwa kisan kiyashi a Iraqi, bayan Mayakan IS sun karbe ikon birane da dama a arewacin kasar cikinsu har da garin Qaraqosh mai yawan mabiya addinin Kirista.

Mayakan IS sun tursasawa daruruwan Kirista ficewa daga Qaraqosh bayan karbe ikon garin tare da kona wuraren ibadarsu.

Tuni Firaministan Birtaniya David Cameron ya yi na’am da matakin Amurka na yin amfani da karfi domin murkushe Mayakan IS.

Amurka zata fara tura jirgin yakinta mai suna Armada dauke da abinci da ruwa zuwa ga daruruwan mabiya Yazidi da Mayakan IS suka kora daga gidajensu a Mosul.

Obama yace Amurka zata kaddamar da hare hare ta sama akan Mayakan IS idan har suka tunkari garin Arbil inda Amurka ta jibge Jami’anta da ke aikin bayar da horo ga dakarun Iraqi.

A karshen watan Yuni ne Mayakan IS da ke adawa da gwamnatin Shi’a a Iraqi suka ayyana kafa daular Islama tare da karbe ikon wasu yankunan Iraqi da Syria.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.