Isa ga babban shafi
Faransa-Mali

An yi zaman makokin 'yan jaridar RFI 2 da aka kashe a Mali

A jiyane aka gudanar da zaman makokin yan jaridun Radiyon Faransa 2, da aka kashe a kasar Mali. Zaman makokin girmama mamatan 2, Ghislin Dupont da Claude Verlon an gudanar da shi ne a gidan ajiye kayan tarihi na Quai Branly dake birnin ParisA lokacin Zaman makokin da aka gudanar a bayanar jama’a ‘yan uwa da aminan arrziki tare da shuwagabanni sun gudanar da jawabai,Shugabar gungun kafafen yada labaran Fransa dake yada labarai a kasashen Ketare, Marie-Christine Saragosse ta karanta wata wasika ne ta nuna alhini da shugaba Hollande ya aika mata.Anasa bangare ministan harakokin wajen kasar Faransa Laurent Fabius, ya bayyana a cikin ko wane irin hali sun goyon bayan kafofin yada labaran kasarZaman makokin na jiya ya samu halartar ministan yada labaran kasar Mali Jean-Marie Idriss Sangare wanda ke cewaKasar Mali na Tarayya a cikin alhinin mutuwar ‘yan jaridar, ganin cewa an saba rayuwa tare, yau kuma ga wadan kujeru 2 da babu kowa a kai. 

'Yan jaridar RFI da aka kashe a Mali, Ghislin Dupont da Claude Verlon
'Yan jaridar RFI da aka kashe a Mali, Ghislin Dupont da Claude Verlon RFI / PIERRE RENE-WORMS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.