Isa ga babban shafi
Fransa

Gawarwakin wakilan RFI da aka kashe a Mali sun isa birnin Paris

A safiyar yau talata ne, aka isa birnin paris na kasar Faransa da gawarwakin Ghislaine Dupont da kuma Claude Verlon, ma’aikatan rediyo Faransa RFI da aka kashe a garin Kidal na arewacin Mali.

Gawarwakin Ghislaine Dupont da Claude Verlon lokacin da aka isa da su a filin jirgin sama na Roissy-Charles-de-Gaulle, ce mardi 5 novembre, à 6H00 TU.
Gawarwakin Ghislaine Dupont da Claude Verlon lokacin da aka isa da su a filin jirgin sama na Roissy-Charles-de-Gaulle, ce mardi 5 novembre, à 6H00 TU. AFP PHOTO / FRED DUFOUR
Talla

An dai isa da gawarwakin ne a filin sauka da tashin jiragen sama na Roissy da ke Paris da misalin karfe 7 na safe, inda aka sauko da gawarwakin a gaban idon manyan jami’an gwamnatin Faransa da suka isa filin saukar jiragen saman.

A can kuwa birnin Bamako fadar gwamnatin Mali, shugaban kasar Ibrahim Boubakar Keita, ya bayar da lambobin yabo na girmamawa ga marigayen dangane da rawar da suka taka a fagen yada labarai a cikin Mali da kuma sauran kasashen duniya kafin su hadu da ajalinsu a ranar asabar da ta gabata a cikin kasar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.