Isa ga babban shafi
Faransa

Gwamnatin Faransa ta zargi ‘yan ta’dda da kisan wakilan RFI

Gwamnatin Kasar Faransa ta ce ‘Yan ta’adda ne suka kashe ma’aikatan tashar Rediyo Faransa a kasar Mali, kamar yadda Ministan harkokin wajen kasar Laurent Fabius ya sanar. 

Wakilan Radiyo Faransa da aka kashe Mali a karshen makon da ya gabata
Wakilan Radiyo Faransa da aka kashe Mali a karshen makon da ya gabata 路透社
Talla

Fabius ya ce, an yiwa ‘Yan Jaridun Ghislane Dupont da Claude Verlon kisan gilla ne, a dai dai lokacin da suke gudanar da ayyukansu.

Shugaban kasar Faransa, Francois Hollande ya gudanar da wani taron manyan jami’an sa kan lamarin.

Mataikiyar shugabar Gidan Rediyo Faransa, Cecile Megie, ta bayyana kaduwar ta da kisan ta kara da cewa daukacin ma’aikatan tashar sun nuna kaduwarsu suma da jimami.

Hukumomin tashar sun kara da cewa ya kamata a sani cewa ‘yancin aikin jarida wani abune da ya rataya a wuyansu inda ya zama dole a sanar da mutane lamarin da ake ciki.

A yanzu haka rahotanni na nuni da cewa an debo gawawwakin mutanen biyu an kais u wani asibiti dake birnin Bamako domin gudanar da bincike.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.