Isa ga babban shafi
Rasha-Amurka

Rasha ta zargi Amurka akan kudirin Syria

Kasar Rasha ta zargi Amurka da yunkurin bata mata suna dan amincewa da kudirin Majalisar Dinkin Duniya mai tsauri kan kasar Syria. Ministan harkokin wajen kasar, Sergei Lavrov ya bayyana haka, inda ya ke cewa, Amurkawan sun sanar da cewar idan Rasha ba za ta goyi bayan kudirin Majalisar Dinkin Duniya ba, zasu janye daga aikin da suke a hukumar hana yaduwar makamai masu guba.

Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry tare da Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov
Sakataren harakokin wajen Amurka John Kerry tare da Ministan harakokin wajen Rasha Sergei Lavrov
Talla

Lavrov yace, idan kawayen su ya rufe kan dole sai an kawar da shugaba Bashar al Assad daga karaga, don nuna karfinsu, amma ba wai don warware matsalar makami mai guba da ke gabansu ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.