Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Hukumar kare hakin bil'adama ta Human Right Watch nada bukata ga Amurka da Rasha.

Hukumar kare hakkin bikl’adama ta Human Right Watch tayi kira ga Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da na Rasha Sergei Lavrov da su taimakawa Tawagar masu tantance yadda ake keta hakkin bil’adama isa kasar ta Syria mai fama da yaki.

Hatimin Human Right Watch
Hatimin Human Right Watch
Talla

Dama dai sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry da na kasar Rasha Sargie Lavrov na a Geneva ne domin tattauna matakan da suka kamata a dauka kan matsalar kasar Syria.

Hakama suna tattaunawa ne domin cire kasar Syria daga jerin kasashe masu Makamai masu Guba a Duniya, kazalika da hana kai harin da kasar Amurka ke yiwa kasar ta Syria, bisa zarginta da amfani da Makamai masu Guba.

Sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry yayi bayanin matsayin amurka a wannan taron.

Yace zan fada cewar a madadin gwamnatin Amurka shugaba Obama, ya himmatu ainun kan tattaunawar da zata kaiga samun maslaha kan kasar Syria, kuma mun san cewar manufarmu guda da Rasha.

Mun hada Hannayen mu domin cimma manufa guda da zata kai mu ga cika burin mu.
Mun kuma tattauna kan wasu ayukan da zamuyi a kasashen mu daban-daban mu sake haduwa a Newyork lokacin babban taron Majalisar dunkin Duniya.

Shugaban hukumar kare hakkin bil’adama ta majalisra dunkin Duniya Remigiusz Henczel yace ya kamata masu tattaunawar su lura da yanda ya kamata su taimakawa Tawagar masu sa Ido kan keta hakkin bil’adama isa kasar ta Syria mai fama da fada tsakanin ‘yan tawaye da Sojin gwamnati.

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ‘yan tawayen kasar ta Syria ke nasu taron domin duba yanda zasu kafa gwamnatin rikon kwarya a kasar ta Syria a yayin da shugaba Bashar al-Assad ke ci gaba da shugabancin kasar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.