Isa ga babban shafi
Syria-MDD

Sakaraten harkokin wajen Amurka ya gana da takwarorinsa na Faransa da Birtaniya

Kasashen Birtaniya da Faransa da kuma Amurka, na ci gaba da yin kashedi ga kasar Syria domin ta mutunta yarjejeniyar da aka cimma na mika makamanta a karkashin kulawar kasashen duniya inda daga baya za a lalatasu.

Sakataren wajen Amurka Kerry, da Hague Birtaniya da kuma Fabius na Faransa
Sakataren wajen Amurka Kerry, da Hague Birtaniya da kuma Fabius na Faransa REUTERS/Charles Platiau
Talla

Ministocin harkokin wajen kasashen uku, sun yi wannan kira ne a wajen wata ganawa da suka yi a Birnin Paris.

Wannan matsaya da Amurka da Faransa da Birtaniya suka dauka na zuwa ne bayan Amurkan da Rasha sun cimma yarjejeniyar yadda za a yi da makaman Syria masu guba, inda suka ja kunnen kasar da kada ta kuskura ta kaucewa yarjejeniyar da aka yi, kuma Sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Kerry ne, ya fara yin kashedi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.