Isa ga babban shafi
Syria

Har yanzu Faransa da Rasha na samun sabani game da batun Syria

Rahotanni na nuna cewa har yanzu kasashen Faransa da Rasha na ci gaba da samun sabani game da batun yadda za a yi da makaman Syria masu guba yayin da ake shirin yin wata mahawara a zauren Kwamitin tsaron Majalisar Dinkin Duniya game da batun.

Daga Dama- John Kerry na Amurka, Laurent Fabius Faransa da William Hague na Birtaniya
Daga Dama- John Kerry na Amurka, Laurent Fabius Faransa da William Hague na Birtaniya REUTERS/Charles Platiau
Talla

Bayan wata ganawa da suka yi a birnin Moscow, Ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergie Lavrov da takwaransa na Faransa, Laurent Fabius sun bayyana sabanin dake tsakanin kasashen game da batun Syria.

“Duk da cewa mun dauki matsaya daya game da batun lalata makaman Syria masu guba, mun samu babanci ra’ayi game da yadda za a cimma hakan.” Inji Lavrov.

Duk da cewa rahoton Majalisar Dinkin Duniya ya nuna cewa an yi amfani da makamai masu guba a Syria “ babu shidar da za ta nuna cewa gwamnatin Assad ce ta yi amfani da makaman.”

To sai dai Fabius ana shi bangaren cewa ya yi “ tabbas rahoton majalisar na nuna cewa hukumomin Damascus ne suka yi amfani da makaman.”
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.