Isa ga babban shafi
Pakistan-Amurka

Pakistan ta kalubalanci Obama game da amfani da kuramen jirage

Gwamnatin Pakistan ta jaddada matsayinta na kalubalantar amfani da kuramen jirage a yankunanta sun saba wa doka, bayan Shugaba Barack Obama ya kare kudirin Amurka na amfani da jiragen tare da fito da sabbin hanyoyin aiki da su.

Samfarin Kuramen jiragen Saman Amurka
Samfarin Kuramen jiragen Saman Amurka REUTERS/U.S. Air Force/Lt Col Leslie Pratt
Talla

Lauyoyin Majalisar Dinkin Duniya da ke binciken sahihancin amfani da jiragen sun yaba da kalaman Obama a lokacin da shugaban ke jawabi game da yaki da ta’addanci a Amurka.

Obama ya sha alwashin ci gaba da amfani da jiragen amma yace dole sai an yi taka tsantsan wajen kai hare haren domin kaucewa rayukan fararen hula.

A wani bincike da Lauyan Majalisar Dinkin Duniya Ben Emmerson suka gudanar sun ce Amurka ta kai hare haren kuramen jirage 25 a kasashen Pakistan da Afghanistan da yankunan Falesdinawa da kuma Somalia, wanda suka ce kalubale ne ga dokokin duniya.

Kodayake gwamnatin Pakistan ta yaba da wasu kalaman Obama inda yace amfani da karfi ba zai kawo zaman lafiya ba, amma ta soki kalaman Obama game hare haren sama da ake kai wa a yankunan arewa maso yammacin kasar.

A jawabin Obama, shugaban yace Amurka zata ci gaba da amfani da jiragen yakinta domin kariya daga hare hare.

A wani sakamakon bincike, mutane kimanin 3,587 jiragen yakin Amurka suka kashe a Pakistan tun a shekarar 2004.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.