Isa ga babban shafi
MDD

MDD tana nazarin kafa dokar amfani da kuramen jirage

Jakadan Majalisar Dinkin Duniya na musamman a fannin yaki da ta’addanci da kare hakkin Bil adama, ya kaddamar da wani bincike akan barnar da kuramen jirage, wato jiragen yakin da basa dauke da matuki, ke yi akan fararan hula domin tabbatar da hukunci akan yin hakan.

Wasu Samfarin kuramen Jirage Birtaniya
Wasu Samfarin kuramen Jirage Birtaniya Pascal Rossignol / Reuters
Talla

Ben Emerson wanda Lauya ne, ya ce kamar yadda aka fitar da wannan fasahar yaki ta yin amfani da kuramen jiragen, ya kamata a fitar da wata doka ta musamman da za ta hukunta duk wanda ya yi amfani da ita ta hanyar da bai kamata.

Jakadan ya ce, bincike da aka fara zai mayar da hankali ne akan wasu hare hare da aka kai guda 25 akan kasar Pakistan ta hanyar amfani da fasahar kuramen jirage.

Akalla fararen hula sama da 3000 ire-iren wadannan hare hare suka kashe a Pakistan a shekarar 2004 cikinsu har da yara kanana 176.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.