Isa ga babban shafi
Pakistan

Jerin hare hare sun kashe Mutane sama da 100 a Pakistan

Akalla mutane 115 aka ruwaito sun mutu a Pakistan sanadiyar wasu jerin hare hare da aka kai a sassan yankunan kasar. Rahotanni sun ce mutane 81 suka mutu a yankin Kudu maso Yammacin birnin Quetta. Kuma an dangata hare haren a matsayin rana mafi muni da aka fi zubar da jini a Pakistan cikin shekaru masu yawa.

Harin da aka kai a yankin Quetta, kasar Pakistan
Harin da aka kai a yankin Quetta, kasar Pakistan REUTERS/Naseer Ahmed
Talla

A kwanan baya Pakistan ta fuskanci hare hare daga jiragen yakin Amurka da suka kai wa ‘Yan kungiyar Taliban inda hare haren suka kashe mutane akalla Biyar.

Wani Jami’in ‘Yan Sanda Zubair Mehmood, yace an kai harin ne ga mabiya Shi’a a Baluchistan wanda ya kashe mutane 81.

‘Yan Sandan kasar sun ce akwai ‘Yan jaridu da ma’aikatan agaji da harin ya rutsa da su.

Tuni dai Kungiyar ‘Yan Sunni masu tsauri ta Lashkar-e-Jhangvi, ta dauki alhakin harin da aka kai a jiya Alhamis.

Kafin kai wa ‘Yan Shi’a harin, an fara kai wa wasu Jami’an tsaro hari ne a Quetta wanda ya kashe mutane 12 tare da raunata wasu mutane 40.

Wata kungiyar ‘Yan tawaye da ake kira Baluch Army sun fito sun yi ikirarin kai harin.

Wani babban Jami’in ‘Yan sanda ya tabbatar da wani hari da aka kai wa ‘Yan Sunni a yankin Arewa maso Yammacin Mingora wanda ya kashe mutane 22 tare da raunata wasu mutane 70. Babu dai wata kungiya da ta fito ta yi ikirarin kai harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.