Isa ga babban shafi
Pakistan

‘Yan sandan Pakistan sun tarwatsa gangamin masu zanga-zanga a Islamabad

‘Yan sandan Pakistan sun harba hayaki mai sa hawaye domin tarwatsa masu zanga-zanga a birnin Islamabad, inda dubban mutane suka amsa kiran Malamin Addini Tahir-ul Qadri domin nuna adawa da gwamnatin kasar.

Muhammad Tahir ul-Qadri Jagoran gangamin adawa da gwamnati a kasar Pakistan
Muhammad Tahir ul-Qadri Jagoran gangamin adawa da gwamnati a kasar Pakistan REUTERS/Mohsin Raza
Talla

Malamin wanda aka zarga da yunkurin haifar da tashin hankalin Siyasa kamin gudanar da zabe a kasar Pakistan, ya jagoranci Dubban Daruruwan mutane ne domin gudanar zanga-zangar neman sauyi a Islamabad.

Tahirul Qadri ynaa zargin gwamnatin kasar ne da haifar da cin hanci da karban Rashawa da gazawa wajen tafiyar da Gwamnati.

Malamin ya cusawa mutane bukatar samar da sauyi ta hanyar kafa gwamnatin rikon kwarya kamin gudanar da zabe.

Malamin yayi Ikrarin yin gangamin da zai samu halartar akalla mutum miliyan Biyu, yana mai cewar magoya bayansa za su fito da shirin su ta hanyar tanadin kayan abinci, da man Fetir, da Barguna su tsaya Daram a sansanin zanga-zanga har sai bukatar su ta biya.

Wasu jami’an tsaro sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar masu zanga-zangar sun kai mutum dubu 500.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.