Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake harba makamai masu linzame guda uku

Kasar Korea ta Arewa ta harba wasu sabbin makamai masu linzame guda uku masu cin dogon zango wadanda suka fada a cikin tekun kasar Japan a sanyin safiyar yau asabar.

Tauraron Korea ta Arewa (KSLV-I satellite)
Tauraron Korea ta Arewa (KSLV-I satellite) AFP
Talla

Ministan tsaron kasar ta Korea, ya bayyana harba makaman da cewa wani bangare ne na atisaye da sojojin kasar ke gudanarwa a daidai lokacin da wasu kasashe ke yi wa kasarsa barazana a cewarsa.
Ministan tsaron ya ce ko baya ga wadannan makamai guda uku da aka harba a safiyar yau, a ci gaba da gudanar da wannan atisaye dakarun kasar na shirin harba wasu makaman a marecen yau
Tun a cikin watan Fabarairun da ya gabata ne dai, Korea ta Arewa ta shiga takun saka tsakaninta da kasashen Amurka, Korea ta Kudu da kuma Japan sakamkon wani atisayen hadin gwiwa da sojojin kasashen suka yi a kusa da gabar ruwanta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.