Isa ga babban shafi
Syria-Isra'ila-Amurka

Obama da Erdogan sun yi kira ga Assad da ya yi murabus

Shugaban kasar Amurka Barack Obama da Firaministan Turkiya, Recep Tayyip Erdogan sun jaddda bukatarsu ta sai shugaban Syria Bashar al Assad ya yi murabus domin kawo karshen zubar da jinni a kasar.  Obama ya ce babu wata Dubara ko asiri da za,a yi amfani domin kawo karshen rikicin Syria.  

Shugaban kasar Amurka, Barack Obama da takwaransa na Turkiya Recep Tayyib Erdogan
Shugaban kasar Amurka, Barack Obama da takwaransa na Turkiya Recep Tayyib Erdogan www.channelnewsasia.com
Talla

A cewar Obama babu wata dabara da za a bi domin warware matsalar rikicin.

“Babu wata dabara da za’a bi domin warware halin rikicin da ake ciki a Syria, inda akwai da mun tattauna tsakanin na da Firaministan Turkiya, amma zamu nemi goyon bayan kasashen Duniya domin karfafawa ‘yan tawaye don samun sauyin gwamnati a Syria.” Inji Obama

Shugabannin biyu sun yi wannan kira a dai dai lokacin da ake yunkurin samar da damar tattaunawa da gwamnatin ta Assad da ‘yan tawayen kasar a wata mai zuwa.

A yau ne dai ake sa ran Shugaban Rasha Vladimir Putin, zai gana da Ban Ki- moon game da rikicin na Syria.

Shugabannin duniya sun dade suna matsin lamba akan kasar Rasha da ta yi kira ag Assad da ya nemi ‘Yan tawayen sun sansanta.

A daya bangaren kasar Jordan na shirin gudanar da taron kawayen kasar ta Syria a mako mai zuwa inda ake sa ran Ministocin harkokin wajen kasashe 11 za su halarci taron da suka hada da Masar, Qatar, Amurka, Birtaniya, Faransa, Turkiya da kuma kasar Jamus.

A yanzu haka rikicin na Syria an bayyana cewa ya lakume rayukan mutane sama da 94,000.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.