Isa ga babban shafi
Nijeriya,Bauchi

‘Yan adawa sun soki dokar hana fita a Bauchi

Sanya dokar hana fita a wasu sassan jihar Bauchi da ke arewacin Najeriya na ci gaba da haifar da cece-kuce tsakanin jam'iyyun adawa, wadanda ke ganin hakan wani yunkuri ne na yin magudin zabe a jihar.

Hotan Janar Muhammadu Buhari à Kano
Hotan Janar Muhammadu Buhari à Kano REUTERS/Goran Tomasevic
Talla

Dan takarar mukamin Gwamna a Jamiyar adawa ta APC Barrister Muhammad Abubakar ya ce daukar wannan mataki a daidai wannan lokaci da ake dakon sakamakon zabe na nuna cewa da walakin.

‘Babu wani dalilin da zai sa a kafa wannan doka, illa dai watakila ana da wani nufi na kokarin canza sakamakon wannan zabe da karfin tsiya’ a cewar Barrister Muhammad.

A cewarsa abin da ba su sani ba shi ne amfani da na’ura card reader da kuma amfani da shafin internet, magudin zabe a wannan karon ba zai samu gurbi ba.

Gwamnatin Jihar Bauchi dai tace sanya dokar hana fita ya zama dole saboda barazanar tsaro da halin zullumin da aka shiga sakamakon hare-hare Kungiyar Boko Haram.

Wakilinmu Shehu Saulawa ya ruwaito cewa a ranar Assabar da ta gabata, dakarun hadin gwiwar sojoji da ‘yan sanda sun kwashe yini guda suna artabu da gungun ‘Yan bindiga a cikin jerin motoci 10.

Dokar hana fita ta sa’o’i 24 ta shafi kananan hukumomin Bauchi da Kirfi da Alkaleri, inda hare-hare ‘yan bindiga ya fi tsananta, kuma an shawarci jama’a da su kasance a cikin gidajensu, har zuwa lokacin da abubuwa za su daidaita.

Shehu saulawa ya rawaito cewa jirage sojin najeriya sun ta yin shawagi a garin Bauchi inda ake ci gaba da zaman zulumi da tararrabi kan halin da Jihar ta tsinci kanta a ciki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.