Isa ga babban shafi
Najeriya

Obasanjo ya gargadi mikawa soja ragamar Mulki a Najeriya

Tsohon Shugaban Najeriya Olusegun Obasanjo yayi gargadi dan kaucewa duk wani yunkurin mikawa soja ragamar tafi da mulkin kasar kamar yadda yace yanzu haka ana kitsawa.

Tsohon Shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo
Tsohon Shugaban kasar Najeriya Olusegun Obasanjo AFP / Seyllou
Talla

Obasanjon yace bayan tsallake shingen gwamnatin rikon kwarya yanzu haka ana ta rade radin mikawa soja ragamar mulki wanda hakan karan tsaye ne ga kundin tsarin mulkin Najeriya, kuma kasashen duniya ba zasu yarda da haka ba.

Tsohon shugaban yace duk wata gwamnati da zata zo ba ta hanyar da kundin tsarin mulki ya amince da shi ba to ba zata samu wurin zama ba.

Obasanjon ya kuma yaba da rawar da shugaban Amurka Barack Obama, da shugaban kasar Ghana da kuma kungiyar ECOWAS suke takawa na ganin an gudanar da karbaben zabe a Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.