Isa ga babban shafi
Nigeria-ICC

Kotun ICC ta karbi koken da aka shigar kan mai dakin shugaban Najeriya

Kotun Hukunta manyan laifuka ta duniya, ta sanar da karbar korafin Jam’iyyar adawa ta APC ta Najeriya, kan kalaman uwargidan shugaban kasar Patience Jonathan tayi, na kira a jefi duk wanda yace chanji a cikin kasar.Mai gabatar da kara Fatou Bensouda tace suna nazari kan korafin kuma zasu gudanar da binciken da ya dace.Mai Magana da yawun ofishin yakin neman zaben, dan takarar shugabancin kasar, karkashin jam’iyyar ta APC Garba Shehu ya tabbatar da samun wasikar kotun kan korafin da suka gabatar mata.A farkon wannan watan, mai dakin shugaban kasar, dake gudanar da yakin neman zabe a garin Kalaba, ta nemi magoya bayan jam’iyyar su jefi duk wanda yayi taken canji a kasar, wanda shine lakabin jam’iyyar ta APC.Wannan na zuwa ne bayan da manyan ‘yan takarar shugabancin kasar su 2, Janar Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC, da Shugaba mai ci Goodluck Jonathan na PDP, sun sanya hannu kan yarjejeniyar gudanar da yakin neman zabe cikin lumana. 

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, tare da mai dakin sa Patience
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan, tare da mai dakin sa Patience REUTERS/Stringer
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.