Isa ga babban shafi
Najeriya

An yi zaben gwaji a wasu jihohin Najeriya

A Nigeria, matsalolin tantance yatsun masu kada kuri’a daga na’ororin Card Reader, da kuma karancin fitowar jama’a na cikin abubuwan da suka bayyana a zaben gwajin da hukumar zabe ta INEC ta gudanar a wasu jihohion kasar 12. Wakilinmu Shehu Saulawa daya bi diddigin zaben gwajin a garin jama’are na jihar Bauchi, yace jami’an hukumar zaben sun tattara wadannan matsaloli, a matsayin abubuwan da za a magance kafin zaben na ainihi, a karshen watan nan.Sai dai duk da wannan, hukuamr zaben tace ba gudu, ba ja da baya wajen amfani da na’urar ta Card Reader, a zabukan na ranakun 28 ga wannan watan, da kuma 11 ga wata mai zuwa na Aprilu.A game da matsalar da aka samu wajen tantance yatsun jama’a a wasu wuraren, hukumar tace na’ura na samun matsala ne wajen tantance yatsun mutun in har akwai maiko ko datti a hannun.A ranar Laraba mai zuwa shugaban hukumar ta INEC Attahiru Jega, zai gana da kwamishinonin zaben jihohin kasar, inda ake sa rai zasu tattauna kan zaben na gwaji, da kuma amfani da katin zabe na din din din, yayin zabukan masu zuwa.A halin kuma da ake ciki, hukumar ta INEC ta kara wa’adin karbar katunan na din din din, daga ranar 8 ga wannan watan na Maris, zuwa 22 ga wata.Hukumar tace zuwa yanzu kashi 80.3 cikin 100 na ‘yan kasar sun karbi katin zaben nasu. 

Shugaban hukumar Zaben Najeriya attahiru Jega
Shugaban hukumar Zaben Najeriya attahiru Jega Bizwatch
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.