Isa ga babban shafi
Najeriya

Cibiyar NDI ba ta son a sake dage zaben Najeriya

Shugabannin Cibiyar Raya Demokradiyya a duniya National Democratic Institute, su 14 tsoffi da na yanzu, sun bukaci hukumomi a Tarayyar Najeriya da su tabbatar da cewa an gudanar da zabe a ranar 28 ga watan Maris kamar yadda aka tsara.

Shugaban Najeriya mai ci Goodluck Jonathan na Jam'iyyar PDP da babban mai adawa da shi tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya mai ci Goodluck Jonathan na Jam'iyyar PDP da babban mai adawa da shi tsohon Shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari. Reuters
Talla

A sanarwar da suka sanya wa hannu mutanen 14 cikinsu har da tsoffin shugabannin kasashe, ministoci da kuma ‘yan Majalisu, sun ce a matsayin Najeriya kasa mai yawan jama’a da kuma karfin tattalin arziki a Afirka, ya kamata kasar ta kasance abin misali ga sauran kasashe wajen mutunta tsarin dimokuradiyya.

Saboda haka ne mutanen suka bukaci gwamnatin Najeriya da hukumar Zabe INEC da su tabbatar da cewa ba a sake dage zaben shugaban kasa da na ‘yan majalisun Tarayyar ba kamar yadda aka shata 28 ga wannan wata na Maris da kuma zaben jihohi a ranar 11 ga watan gobe na Afrilu.

A wani bangare na sanarwar, manyan jami’an sun bukaci hukumomin tsaron Najeriya wadanda a baya suka ce ba za su iya samar da tsaro ga zaben ba, da su kara azama domin samun nasarar zabukan ma su zuwa.

Jami’an tawagar sa ido a zaben sun kuma shawarci ‘yan takara da su ja kunnan magoya bayansu domin kaucewa tashe-tashen hankula a lokacin zaben kamar dai yadda suka nemi kafofin yada labarai da su yi taka-tsantsan a lokacin zaben.

Daga cikin wadanda suka sanya hannu a wannan sanarwar har da Madeleine Albright tsohuwar sakatariyar harkokin wajen Amurka, da tsohon Firaministan Canada Joe Clark, da tsohon shugaban Botswana Ket Masire da takwaransa na Cape Verde Antonio Monteiro.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan na neman wa'adi na biyu karkashin Jam'iyyarsa ta PDP da ke fuskantar babban kalubale daga Dan takarar Jam'iyyar adawa ta APC Janar Muhammadu Buhari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.