Isa ga babban shafi
Nigeria

MDD ta gargadi Najeriya a kan Zabe.

Majalisar dinkin duniya, ta gargadi Najeriya game da sake dage zabuban kasar, da aka shirya gudanawar tun a farko a watan nan na Fabairu, yayinda daga bisani, aka dage zuwa watan Maris mai zuwa

Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon
Sakatare Janar na Majalisar Dinki duniya Ban Ki-moon REUTERS/Faisal Al Nasser
Talla

Sakatare janar na Majalisar ne, Ban ki-Moon ya bayyana gargadi tare da kira bisa kaucewa rikicin bayan zabe.

Kamar yadda hukumar zabe mai zaman Kanta ta Kasar, ta sanar da saban jadawalin g zaben, Ban, ya ce ga hukumar, da ta tabbatar da rashin sake sauya lokacin da ta bayyana za ta gudanar da zaben.

A dayan bangaren kuwa, Ban ya yi kira ta musamman ga shugabannin siyasar Kasar, da su guji furta kamlaman da kan iya tayar da tarzoma, kana ya yi Allah wadai da duk wata kalma da magoya bayansu kan iya furtawa da nufin hargitsa tsarin gudanar da zaben.

Har ila yau, Sakataren Majalisar, ya aiko jakadarsa na musaman, Mohamed Ibn Chambas, birnin tarayya Abuja, da nufin tattaunawa dangane da zabukan,inda kuma zai yi batun Boko Haram tare da Mahukuntan Kasar.

Dage zabukan na zuwa ne sakamakon matsalar tsaro da kungiyar Boko Haram ta haddasa, kamar yadda hukumar zaben ta bayyana kenan.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.