Isa ga babban shafi
Najeriya

Sojin Najeriya sun kashe Boko Haram 300

Ma’aikatar Tsaron Najeriya tace ta yi nasarar kashe mayakan Boko Haram sama da 300 tare da kwace garuruwa 11 da ke hannun Mayakan a Jihar Borno bayan kaddamar da yaki akansu a cikin mako guda.

Janar  Olukolade Kakakin rundunar Sojin Najeriya
Janar Olukolade Kakakin rundunar Sojin Najeriya Nigeriantribune
Talla

Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron kasar Manjo Janar Chris Olukolade ya sanar da haka inda ya ke cewa sun kwace tarin makamai daga hannun kungiyar.

Jami’in ya ce Mayakan sun kashe sojoji biyu yayin da wasu 10 suka samu raunuka.

Sojojin Najeriya sun karbe ikon garuruwan Mongono da Marte da ke cikin Jihar Borno da Mayakan Boko Haram suka kwace a ranar 25 ga watan Janairu.

A cikin wata sanarwa, Janar Olukolade ya ce sun kuma karbe wasu kauyuka da ke yankin.

Boko Haram dai ta kwace garuruwa da dama a Jihohin Borno da Yobe, tare da kashe dubban mutane a yankin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.