Isa ga babban shafi
Kamaru

Sojojin Kamaru sun kashe ‘Yan Boko Haram 86

Sojojin Kamaru sun kashe ‘yan Boko Haram kimanin 86 tare da kama wasu mutane 1,000 da ake zargi suna da alaka da kungiyar, kamar yadda rundunar Sojin kasar ta tabbatar. Wannnan na zuwa ne a yayin da shugabannin Kasashen tsakiyar Afirka suka yi alkawarin bayar da tallafin kudi Dala miliyan 87 don yaki da kungiyar Boko haram a wani taro da suka yi a Kamaru.

Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya
Sojojin Kamaru da ke yaki da Boko Haram na Najeriya AFP PHOTO / ALI KAYA
Talla

Ma’aikatar tsaron Kamaru tace an kashe Sojojin kasar 5 a musayar wutar da suka yi da ‘yan Boko Haram a yankin Waza da ke kan iyaka da Najeriya.

Kungiyar Boko Haram dai ta fadada hare-harenta zuwa kasashen Kamaru da Chadi da Nijar da ke makwabtaka da Najeriya.

Akan haka ne shugabannin kungiyar kasashen tsakiyar Afrika suka gudanar da taro a Kamaru domin tattauna yadda za su taimaka a dakile ayyukan kungiyar kafin su tsallaka zuwa kasashensu.

Shugabannin da suka halarci taron a Yawunde sun hada da Idriss Deby na Chadi da Catherine Samba Panza ta Jamhuriyyar Afrika ta tsakiya da Denis Sassou Nguesso na Congo da Teodoro Obiang Nguema na Equatorial Guinea da kuma Ali Bongo Ondimba na Gabon.

Shugaban Kamaru Paul Biya ya ce ya zama wajibi su magance matsalar Boko Haram.

Tuni kasashen Chadi da Kamaru da Nijar da Najeriya suka kafa rundunar hadin guiwa domin yaki da Boko Haram.

Kamaru ta ce ta tura mutane 1,000 da ta kama ‘yan Boko Haram zuwa gidan yarin Marwa.

Gwamnatin Nijar kuma tace ta cafke wasu mutane 160 da ta ke zargi suna da alaka da kungiyar Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.