Isa ga babban shafi
Nijar

An cafke ‘Yan Boko Haram da dama a Nijar

Mahukuntan Jamhuriyyar Nijar sun ce ‘Yan Boko Haram da dama ne aka cafke a yankin kudancin kasar, tare da bayyana cewa kimanin mutane 10,000 ne suka tsere daga Diffa zuwa Damagaram saboda barazanar Boko Haram na Najeriya. Gwamnan Jihar Damagaram Muntari Kalla ya ce Jami’an tsaro sun cafke wasu da suke zargi ‘Yan Boko Haram ne da dama, kuma ‘yan asalin kasar Nijar ne.

Dakarun da ke fada da Boko Haram na Najeriya
Dakarun da ke fada da Boko Haram na Najeriya RFI/OR
Talla

Gwamnan ya ce an aika da mutanen sama da 10 zuwa Yamai babban birnin kasar domin bincikensu.

Mayakan Boko Haram sun kaddamar da hare hare a kan iyakokin Najeriya domin mayar da martani ga rundunar hadin guiwa da Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru suka kafa domin yakarsu.

Boko Haram ta kai hare haren a garin Diffa da ke kusa da Najeriya a makon jiya

Mahukuntan Nijar sun ce adadin mutane kimanin 10,000 suka tsere daga Diffa zuwa Damagaram saboda barazanar Boko Haram

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.