Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben 2015: Kotun Koli ta wanke Jonathan

Kotun Kolin Najeriya ta yi watsi da karar da Cyriacus Njoku ya shigar domin neman a haramtawa Shugaba Goodluck Jonathan takarar zaben da za a yi a ranar 28 saboda ya karbi rantsuwar shugabanci sau biyu. Mai shari’a Abubakar Yahya ya bayyana cewar rantsuwar da Jonathan y ayi bayan rasuwar Yar’Adua ba ta cikin lissafi.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da tawagarsa a yakin neman zaben 2015
Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da tawagarsa a yakin neman zaben 2015 REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Njoku ya ruga kotun ne don ganin ta hana shugaban takarar zaben, saboda ya yi rantsuwar kama aiki sau biyu lokacin da ya gaji marigayi Umaru Musa Yar’Adua da kuma lokacin da aka zabe shi a shekarar 2011.

Mai shari’a Abubakar Yahya ya ce Jonathan na da damar tsayawa takara a bana, tare da umurtar Njoku wanda ya shigar da karar ya biya shugaba Jonathan naira 50,000.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.