Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsalar Mai ta fara tsananta a Najeriya

Jam’iyyar PDP mai mulki a Najeriya ta zargi shugabannin Jam’iyyar adawa ta APC da hannu akan matsalar karancin fetir da aka shiga a kasar, a yayin da Matsalar ke ci gaba da tsananta sassan kasar.

AFP / W. Y. Maniengui
Talla

A shafin shi na Twitter Shugaban Jam’iyyar PDP Adamu Mu’azu ya zargi shugabannin APC da hada baki da dillalan man domin haifar da matsalar domin bata wa dan takararsu shugaban kasa Goodluck Jonathan suna.

Sai dai Mu’azu bai ambaci sunayen shugabannin APC da ya ke zargi ba.

Amma a lokacin day a ke mayar da martani, Kakakin Jam’iyyar APC Lai Muhammad ya yi watsi da zargin tare da dora alhakin matsalar ga gwamnatin Jonathan.

Lai Muhammad ya ce babu ruwan APC da matsalar karancin mai, illa gwamnatin PDP ce da ta sace kudaden man.

A cewarsa, gwamnatin PDP ta shiga rudani saboda fargabar shan kaye a zaben mai zuwa.

Ana dai fama da dogayen layukan ababen hawa a gidajen mai musamman a manyan biranen Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.