Isa ga babban shafi
Najeriya

Majalisa: Batun Sojoji a runfunan zabe ya haifar da sabani

An ci cacar-baki tsakanin ‘Yan Majalisar Wakilai game da batun amfani da Sojoji domin samar da tsaro a runfunar zabe, bayan wani kudiri da aka gabatar da ya nuna cewa tura sojojin ya sabawa doka.

Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram
Sojojin Najeriya da ke yaki da Boko Haram AFP/Quentin Leboucher
Talla

A zaman majalisar, an yi cacar-baki tsakanin ‘yan Jam’iyyar PDP mai mulki da kuma APC mai adawa.

Amma ‘Yan Majalisu da dama daga Jam’iyyar APC da ke da rinjaye a Majalisar suna adawa da tura sojoji a runfunar zabe, kamar yadda Femi Gbajabiamila ya gabatar da kudiri da ke cewa amfani da Sojoji a lokacin ya sabawa doka.

Mista Gbajabiamila ya yi la’akari da yadda aka yi amfani da Sojoji a zaben Ekiti aka yi magudi.

Amma bangaren Jam’iyyar PDP a Majalisar sun yi watsi da kudirin, har sai da ta kai suna tada jijiyoyin wuya  da ‘Yan APC a zauren majalisar.

‘Yan majalisa a bangaren PDP sun ce a jingine batun har sai kotu ta yanke hukunci amma bangaren APC na cewa wata Kotu a Sakkwato ta tabbatar da dokar akan Sojoji ba su da hurumi a runfunar zabe illa su kada kuri’a.

‘Yan Majalisar sun ce aikin samar da tsaro a lokacin zabe, hakki ne da ya rataya akan wuyan ‘Yan sanda ba na Soja ba.

A makon gobe ne Majalisa za ta ci gaba da muhawara akan batun.

Masana kundin tsarin mulki sun ce Sojoji ba su da hurumi ga sha’anin zabe, bayan shugaban hukumar zaben Farfesa Attahiru Jega ya shaidawa Majalisa cewa Sojoji ne kawai za su iya bayar da tabbacin ko za a gudanar da zaben a ranar 28 ga watan Maris.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da hedikwatar tsaron kasar sun yi alkawalin za a gudanar da zaben a ranar 28 ga watan Maris kamar yadda aka tsara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.