Isa ga babban shafi
Najeriya

Matsalar Na’ura ta shafi Jonathan

An tantance Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Matarsa a mazabar Otueke Jihar Bayelsa inda Shugaban mai neman wa’adi na biyu zai jefa kuri’arsa. Amma an tantance shugaban ne ba tare da yin amfani da na'urar tantance masu kada kuri’a ba.

An tantance Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Matarsa a mazabar Otueke Jihar Bayelsa a zaben 2015 a Najeriya
An tantance Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan tare da Matarsa a mazabar Otueke Jihar Bayelsa a zaben 2015 a Najeriya REUTERS
Talla

Matsalar na’ura ta sa Goodluck Jonathan da matarsa Patience sun kwashe lokaci suna jiran a tantance su, lamarin da har ya kai aka tantance su ba tare da yin amfani da na’urar ba.

Sau uku ana kokarin tantance Jonathan da na’ura amma ana samun matsala.

Wannan ne karon farko da aka fara amfani da na’ura domin tantance masu kada kuri’a a zaben Najeriya.

Hukumar zaben Kasar ta fito da tsarin amfani da na’urar ne domin maganin magudin zabe.

Goodluck Jonathan ya yi kira ga ‘Yan Najeriya su yi hakuri su bi sabon tsarin na hukumar zabe.

Tuni dai aka tantance Dan takarar Jam’iyyar APC Janar Muhammadu Buhari babban mai adawa da Goodluck Jonathan na PDP.

Rahotanni daga sassan Najeriya na cewa an samu matsalar amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a.

A Jihar Niger sau 10 ana kokarin tantance Gwamnan Jihar Babangida Aliyu amma sai a karo na 11 aka tantance shi.

Baya ga matsalar na’ura an samu tsaikun fara aikin tantance masu kada kuri’a a sassa da dama na Najeriya.

Gwamnan Jihar Rivers Rotimi Amaechi ya bayar da umurnin a dakatar da aikin tantance masu kada kuri’a a karamar Hukumar Ikwerre saboda babu takardar rubuta sakamakon zabe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.