Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Najeriya: Mace mai ciki...

Zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar Assabar a Najeriya, tamkar Mace mai ciki ce ba a san abin da za ta haifa ba, sabanin zabukan da suka gabata a kasar inda ake ganin shugaba mai ci na da yakinin lashe zabe saboda kaurin sunan magudi a Najeriya.

Yarjejeniyar amincewa da matakin kaucewa rikici tsakanin Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari a zaben 2015.
Yarjejeniyar amincewa da matakin kaucewa rikici tsakanin Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari a zaben 2015. Reuters
Talla

Wannan ne karon farko da Jam’iyyar PDP mai mulki ke fuskantar babban kalubale a tarihin zaben Najeriya bayan kawo karshen mulki Soja a 1999.

Shugaba Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP na fuskantar babban kalubale daga dan takarar Jam’iyyar APC mai adawa Tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.

Hukumar Zaben Najeriya ta samar da sabbin sauye sauye a zaben bana domin maganin magudin zabe.

Zagaye na biyu

Akwai yiyuwar zaben zai kai ga shiga zagaye na biyu idan babu dan takara da ya samu kashi 25 daga Jihohin Najeriya 24.

Amma a tarihin siyasar Najeriya ba a taba shiga zagaye na biyu ba a zaben shugaban kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.