Isa ga babban shafi
Najeriya

An kammala yakin neman zabe a Najeriya

An kammala yakin neman zaben shugaban kasa a Najeriya a jiya Alhamis, a yayin da manyan ‘Yan takara suka aiko da sakwanninsu na karshe ga al’umma kafin fara jefa kuri’ar zabe a ranar Assabar. Wannan ne karon farko da Jam’iyyar PDP mai mulki ke fuskantar babban kalubale a tarihin zaben Najeriya.

Tsohon Shugaban Najeriya Janar Abdussalami Abubakar ne ya jagoranci zaman amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari
Tsohon Shugaban Najeriya Janar Abdussalami Abubakar ne ya jagoranci zaman amincewa da yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Goodluck Jonathan da Janar Muhammadu Buhari REUTERS/Stringer
Talla

Shugaba Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP mai mulki da Janar Muhammadu Buhari sun sake sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya don kaucewa tashin hankali a lokacin zabe.

Shugabannin sun amince da yarjejeniyar ne domin kaucewa rikicin da ya faru bayan kammala zaben 2011 inda mutane sama da 1,000 suka mutu.

‘Yan takarar guda biyu sun sake sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya a jiya Alhamis bayan sun amince da yarjejeniyar tun a watan Janairu.

Manyan ‘Yan takarar sun yi kira ga hukumar zabe da jami’an tsaro da su gudanar da ayyukansu kamar yadda dokar kasa ta tanada.

Zaben ranar Assabar ya kasance zabe mafi jan hankali a tarihin Najeriya, inda Shugaba Goodluck Jonathan na Jam’iyyar PDP ke fuskantar babban kalubale daga dan takarar Jam’iyyar APC Tsohon shugaban kasa Janar Muhammadu Buhari.

Tuni dai hukumar zabe a Najeriya ta bayyana cewa ta shirya tsaf domin gudanar da babban zaben a kasar.

‘Yan Najeriya kimanin Miliyan 68.8 ke da ‘yancin kada kuri’a.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.