Isa ga babban shafi
Najeriya

Mazauna Michika sun nemi samun kariya daga Boko Haram

Mazauna garin Michika da ke Jihar Adamawa a tarayyar Najeriya sun bukaci taimakon gwamnatin kasar saboda abin da suka kira yunkurin Boko Haram na kwace garinsu.

Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban Kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau AFP
Talla

Wannan na zuwa ne bayan hare haren da ‘yayan kungiyar suka kai garuruwan Gulak da Michika a karshen mako.

Majiyoyi sun ce dimbin magoya bayan kungiyar dauke da makamai sun afka wa garin ne tun a karshen makon da ya gabata, lamarin da ya sa jama’a suka rika tsere suna barin garin.

Haka zalika wasu rahotanni sun tabbatar da cewa sojojin gwamnati sun samu nasarar kwace garin Bama daga hannun ‘yan kungiyar ta Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.