Kungiyar ECOWAS ta aike da wakilai kusan 40 a matsayin yan sa ido a zabenTogo
A gobe litinin ne ake gudanar da zaben ‘yan majalisar dokokin kasar Togo da na shiyya-shiyya,zaben da ake kalo a matsayin wata hanya ta tsawaita wa’adin mulkin shugaba Faure Gnassingbe a cewar da dama daga cikin yan adawa a wannan kasa.
Wallafawa ranar:
A bisa wannan gyare-gyaren da ‘yan majalisar suka yi gaba daya a ranar 19 ga watan Afrilu 2024, za a zabi shugaban kasa na wa’adin shekaru hudu, wanda za a iya sabunta shi sau daya, ta hanyar yan majalisun za a je zabe kai tsaye.
Yanzu mulki zai kasance a hannun Firaminista wanda dole ne ya zama "shugaban jam'iyyar masu rinjaye" a Majalisar Dokoki ta kasa.
Za a nada shugaban jam'iyyar da ta yi nasara a zaben na ranar Litinin a wannan sabon matsayi. Shugaban jam'iyya mai rinjaye a halin yanzu a Majalisar, Union for the Republic (UNIR), ba kowa bane illa Faure Gnassingbe, wanda ke kan karagar mulki tun a shekara ta 2005 bayan mahaifinsa, wanda shi kansa ya ci gaba da rike madafun iko na kusan shekaru 38.
'Yan adawar na fargabar cewa sabon kudin tsarin mulki zai ba da damar tsawaita wa'adin Faure Gnassingbe a matsayin shugaban kasar.
A jiya Asabar ne aka kawo karshen yakin neman zaben wanda aka soma a ranar 13 ga watan Afrilu.
Hukumar ECOWAS ta aike da wakilai 40 da suka hada da jami'an diflomasiya,alkalai,wakilan kungiyin farraren hula,yan jaridu kamar dai yada Shugaban hukumar Dr Omar Alieu Touray ya sanar.
Tawagar na karkashin shugabancin tsohuwar mataimakiyar shugaban kasar Gambia Fatoumata Jallow-Tambajang.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu