Isa ga babban shafi

Sama da mutane miliyan 50 na cikin barazanar fuskantar yunwa Afrika - Rahoto

Wani bincike da gwamman hukumomin Majalisar Ɗinkin Duniya suka yi a ƙasashe  17 ya nuna cewa sama da mutane miliyan 50 ne za su fuskanci matsalar ciyar  da kansu a yankunan yammaci da tsakiyar nahiyar Afrika a kaka mai zuwa.

Wata mata goye da danta yayin bin layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na wadanda rikicin Tigray ya raba da muhallansu a garin Shire da ke yankin na Tigray.
Wata mata goye da danta yayin bin layin karbar tallafin abinci a sansanin 'yan gudun hijira na wadanda rikicin Tigray ya raba da muhallansu a garin Shire da ke yankin na Tigray. © REUTERS/Baz Ratner/File Photo
Talla

Binciken da aka yi da haɗin gwiwar gwamnatoci da ƙungiyar ƙasashen yammacin nahiyar Afrika ta ECOWAS, an yi shi ne a ƙasashen da suka haɗa da Senegal da Burkina Faso da Mali da Jamhuriya Nijar da Kamaru da kuma Najeriya.

A wannan yanki mai girma, rahoton binciken ya ce mutane miliyan 52 ne za su fuskanci matsala wajen ciyar da kansu da kaka mai zuwa, wato a yayin girbi kenan, tsakanin watan Yuni zuwa Agusta, abin da ke nuni da cewa  an samu ƙarin mutane miliyan 4 da za su shiga wa  wannan hali idan aka kwatanta da na bara.

Rahoton ya yi ƙarin bayanin cewa, kashi 12 na wannan  adadin, ko kuma mutum ciki kowane 10 zai fuskanci matsala wajen samun nau’in abinci mai gina jiki  a yankunan  yammaci da tsakiyar Afrika a wannan lokaci, duba da hasashen da gwamman kungiyoyi, ciki har da Oxfam da Unicef suka yi.

Idan aka ware  ƙasashen Guinea, Jamhuriyar Benin, Ghana da Ivory Coast, ana sa ran ta’azzarar matsalar ƙarancin abinci a dukkannin ƙasashe 17 da aka gudanar da wannan bincike.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.