Isa ga babban shafi

Kenya na jagorancin taron shiga tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu da ƴan tawaye

An fara sabon tattaunawa tsakanin gwamnatin Sudan ta Kudu, da ƙungiyoyin mayaƙan da ba sa cikin yarjejeniyar zaman lafiyar shekarar 2018, wadda ta kawo ƙarshen ƙazamin yaƙin basasar da ya tagayyara ƙasar.

Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka yayin kaddamar da taron shiga tsakanin Sudan ta Kudu da ƴan tawaye a fadar gwamnati da ke Nairobi, Kenya, a ranar Alhamis, 9 ga Mayu, 2024.
Wasu daga cikin shugabannin kasashen Afirka yayin kaddamar da taron shiga tsakanin Sudan ta Kudu da ƴan tawaye a fadar gwamnati da ke Nairobi, Kenya, a ranar Alhamis, 9 ga Mayu, 2024. AP - Brian Inganga
Talla

Taron da Kenya ke jagoranta na gudana ne a Nairobi, babban birnin ƙasar, inda za a ɗora daga inda aka tsaya a tattaunawar neman sulhun ta ƙarshe da ta gudana a shekarar 2019.

Mai masaukin baƙi shugaban Kenya William Ruto ne ya buɗe taron na ranar Alhamis ya bukaci dukkan bangarori da su yi amfani da hikima. 

Ina yi wa baki ɗayan tawagogin da ke halartar wannan taro fatan yin amfani da hikima, da Juriya yayin shawarwarin da za su gabatar.

Ruto ya ce ya yi amannar cewar jagoran masu shiga tsakanin tare da mataimakinsa zasu kaisu ga cimma matsaya karɓaɓɓiya

Babban abinda muka sanya a gaba shi ne samar da dauwwamammen zaman lafiya a Sudan ta Kudu da yakin Gabashin Afirka da ma nahiyar baki ɗaya.

Shi kuwa shugaban Sudan ta Kudu Salva Kirr ya buɗe jawabinsa ne da alkawarin yin dukkanin mai yiwuwa wajen cimma nasarar tabbatar da sulhun da ake nema.

Sudan ta Kudu za ta shiga wannan tattaunawa da  kyakkyawan fata, fatan da muke shi ne suma bangarorin da zamu gana da su kasance tare da kyakkyawar aniyar neman dawo da zaman lafiya a Sudan ta Kudu, nasarar da in aka cimma, za ta samar da daidaito da kuma cigaban tattalin arzikin yankin gabashin afirka, inda kasar tamu take.

Shugaban ƙasar Malawi Lazarus Chakwera da na Zambia Hakainde Hichilema da na Zambiya, Nangolo Mbumba da na Namibia, da Faustin-Archange Touadera na Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya su ma sun halarci bikin kaddamar da taron da aka gudanar bayan wani taron noma na kungiyar Tarayyar Afirka da aka kammala da safiyar Alhamis.

Shugabannin kasashen Afirka da tawagogi, yayin kaddamar da taron shiga tsakanin Sudan ta Kudu da ƴan tawaye a fadar gwamnati da ke Nairobi, Kenya, a ranar Alhamis, 9 ga Mayu, 2024.
Shugabannin kasashen Afirka da tawagogi, yayin kaddamar da taron shiga tsakanin Sudan ta Kudu da ƴan tawaye a fadar gwamnati da ke Nairobi, Kenya, a ranar Alhamis, 9 ga Mayu, 2024. AP - Brian Inganga

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.