Isa ga babban shafi

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa kan harin RSF a yankin Darfur na Sudan

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna matukar damuwarsa kan harin da dakarun sakai na RSF a Sudan suka kai al-Fashir da ke yankin arewacin Darfur.

Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna matukar damuwarsa kan harin da dakarun sakai na RSF a Sudan suka kai al-Fashir da ke yankin arewacin Darfur.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya nuna matukar damuwarsa kan harin da dakarun sakai na RSF a Sudan suka kai al-Fashir da ke yankin arewacin Darfur. AFP - -
Talla

Al-Fashir ne babban birni a yankin Darfur da ba ya karkashin ikon dakarun na RSF, domin tuni da su da kawayenta suka mamaye wasu manyan biranen jihar Darfur hudu a bara, kuma ana zarginsu da kisan gilla kan kungiyoyin da ba na Larabawa ba, da kuma cin zarafi a yammacin Darfur.

Ko a makon da ya gabata, manyan jami'an Majalisar Dinkin Duniya sun gargadi Kwamitin tsaro cewar kimanin mutane 800,000 a al-Fashir na cikin matukar hadari gaggawa yayin ake fargaba sake rikcin kabilanci ya barke a Darfur, saboda yadda RSF ke kashe kabilun da ba larabawa ba.

A shekarar da ta gabata ce, wani sabon yaki ya barke a Sudan tsakanin sojojin gwamnati karkashin janar Abdel Fattah al-Burhan da dakarun sa kai na RSF dake biyeyya ga tsohon mataimakinsa Mohamed Hamdan Dagalo, wanda ya haifar da ƴan gudun hijira mafi girma a duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.