Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kai hari a Gulak da Minchika

Rahotanni daga Najeriya na tabbatar da cewa mutanen garuruwan Gulak da Minchika a Jihar Adamawa da dama ne ke tserewa zuwa Yola da Mubi da wasu wurare daban daban bayan da Mayakan Boko Haram suka abka wa garuruwan. Rahotanni daga Gulak sun ce tun da sanyin safiya ne aka yi musayar wuta tsakanin ‘Yan Boko Haram da Sojojin Najeriya, amma daga baya ‘yan Boko Haram suka fi karfin Sojin na Najeriya, lamarin da ya sa suka tsere zuwa garin Shuwa.

Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram, Abubakar Shekau
Talla

Zuwa yanzu dai babu tabbaci ko Mayakan na Boko Haram sun karbe ikon Gulak bayan sun karbe Madagali a Jihar Adamawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.