Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

Sojojin Kamaru sun kashe Mayakan Boko Haram 40

Ma’aikatar Tsaron kasar Kamaru tace sojojinta sun kashe ‘Yan kungiyar Boko Haram 40 wadanda suka yi kokarin kai hari kan mashigin iyakar kasar da Najeriya. Sanarwar da ma’aikatar ta yi ta gidan radeyoo, taace mayakan dauke da muggan makamai sun yi kokarin ratsa wa ta gadar Fokotol, inda suka bude wuta akan sojojin kasar.

Wasu 'yan kungiyar Boko Haram tare da shugabansu Abubakar Shekau
Wasu 'yan kungiyar Boko Haram tare da shugabansu Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Sanarwar ta kara da cewar zaratan sojojin Kamaru sun mayar da martani inda suka kashe 40 daga cikin Mayakan , yayin da soja guda ya samu rauni.

Wannan na zuwa ne kuma a yayin da Mayakan Boko Haram suka kwace ikonm garin Bama. Kodayake rundunar Sojin Najeriya ta musanta cewa Boko Haram ta karbe Bama.

A makon jiya ne dai Mayakan Boko Haram suka yi ikirarin kafa sabuwar daular Musulunci bayan sun karbe garin Gwoza kafin su karbe Gamboru Ngala.

Masana suna bayyana fargaba akan makomar Najeriya musamman yadda Mayakan Boko Haram ke ci gaba da kwace garuruwa a arewa maso gabacin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.