Isa ga babban shafi
Najeriya

Modu Sheriff: Ban da alaka da Boko Haram

Tsohon gwamnan Jihar Borno Senata Ali Modi Shariff, ya yi watsi da zargin da wani dan kasar Australia mai suna Stephen Davis wanda gwamnatin Najeriya ta nema domin shiga tsakani kan yadda za a ceto ‘yan matan Chibok ya yi ma sa, wanda ya ce tsohon gwamnan da kuma tsohon babban hafsan sojojin Najeriya Janar Azubuike Ihejirika, ke daukar nauyin ayyukan kungiyar Boko Haram.

Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da Senata Ali Modu Sheriff tsohon Gwamnan Jihar Borno
Shugaban Boko Haram Abubakar Shekau da Senata Ali Modu Sheriff tsohon Gwamnan Jihar Borno Nigeriantribune
Talla

A zantawarsa da RFI Hausa, Ali Shariff ya ce zai shigar da kara domin kalubalantar Dr Davis wanda ya yi masa wannan zargi, kafin daga bisani ya yi dirar mikiya akan tsohuwar jam’iyyarsa ta APC da ke fatawar ganin an dauki mataki akansa.

A ranar 28 ga watan Agusta ne Baturen kasar Australia Stephen Davis da ke jagorantar tattaunawa da Mayakan Boko Haram domin kubutar da ‘Yan matan garin Chibok da aka sace a Jihar Borno, ya shaidawa wata Kafar Telebijin cewa Tsohon Gwamnan Jihar Borno Senata Ali Modu Sheriff da tsohon babban hafsan Sojin kasar Janar Azuburike Ihejirika su ke daukar nauyin ayyukan Mayakan Boko Haram.

Dr Davis ya shaidawa kafar Telebijin ta Arise News a London cewa mutanen biyu suna da hannu ga ayyukan Boko Haram a Najeriya tare da kira ga gwamnatin kasar ta kaddamar da bincike akai.

Modu Sheriff yace bai san Boko Haram ba kuma bai taba alaka da su ba.

A cewarsa yana cikin wadanda Boko Haram suka fi yi wa ta’adi domin sun kashe ma sa ‘Yan uwa da abokansa da dama.

Modu Sheriff kuma ya yi watsi da zargin cewa ya nemi taimakon Tsohon shugaban Boko Haram da Sojoji suka kashe Muhammad Yusuf domin samun nasarar zabe a Jihar Borno a 2003.

“Wallahi Tallahi ban taba ganin Muhammed Yusuf ba a rayuwa na sai da Sojoji suka kama shi”, inji Sheriff.

Ya kuma ce zai kalubalanci Dr Davis a Kotu akan bacin sunan da ya yi ma sa.

03:16

Tattaunawa da Sanata Ali Modu Sheriff

Kabir Yusuf

Yanzu haka Mahawara ce ta kaure tsakanin ‘Yan Najeriya kan zargin su Modu Shariff game da Boko Haram musamman Jam’iyun siyasa da suka fara cacar baki akai.

Babbar jam’iyyar adawa ta APC a ta bakin shugabanta Odigie Oyegun, ta yi kakkausar suka ga gwamnatin PDP da ke mulki a Najeriya tare da gaskata dukkanin abin da ke kunshe a hirar da aka yi da Dr Davis, tana mai cewa ya rage kawai ga gwamnatin Tarayyar ta dauki mataki idan dai ba ita ma tana da hannu a ciki ba.

Masu lura da al’amurra a Najeriya dai na ganin cewar ya kamata Jam’iyyar PDP da APC su mayar da hankali ga kokarin magance matsalar Boko Haram da ta zama Tsumagiyar kan Hanya ga al’ummar kasar.

Yanzu haka Mayakan Boko Haram sun yi ikirarin kafa sabuwar daula bayan sun karbe ikon wasu birane a Kudancin Jihar Borno.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.