Isa ga babban shafi
Najeriya

Kaduna: Jonathan ya jajantawa Buhari

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya jajantawa Janar Muhammadu Buhari da Sheikh Dahiru Bauchi da ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a tawayen hare haren bama bamai da aka kai a garin Kaduna.

Motar Janar buhari da aka kai wa harin Bam a Kaduna
Motar Janar buhari da aka kai wa harin Bam a Kaduna facebook
Talla

Shugaba Goodluck Jonathan ya yi Allah wadai da harin da aka kai Kaduna wanda ya yi sanadiyar rasa rayuka da dama.

Akalla mutane 82 aka tabbatar da mutuwarsu a tawayen hare haren da aka kai a Kaduna, kuma yanzu mahukuntan Jahar sun kafa dokar hana fita ta sa’o’I 24.

Da misalin karfe 12: 30 na rana aka fara kai wa Tawagar Sheikh Dahiru Bauchi bayan ya rufe Tafsirin Al Kur’ani mai girma a watan Azumin Ramadan.

Mutane kimanin 50 Jami’an agaji na Red Cross suka tabbatar da mutuwarsu a hari na biyu da aka kai wa Tawagar Janar muhammadu Buhari tsohon Shugaban Najeriya.

A cikin wata Sanarwa Buhari yace an nemi a kashe shi ne.

Janar Muhammadu Buhari, ya yi Allah wadai da harin, kuma yace hakan ba zai hana shi fadin gaskiya ba ko sauya matsayinsa ba, kamar yadda na hannun damansa kuma tsohon Dan Majalisar wakilai Hon Faruk Adamu Aliyu ya shaidawa RFI Hausa.

A cikin wata Sanarwa, mai ba shugaban Najeriya shawara kan harkokin yada labarai Reuben Abati ya jajantawa Janar Muhammadu Buhari da Sheikh Dahiru Bauchi da kuma ‘yan uwan wadanda suka rasa rayukansu a tawayen hare haren.

Wadannan hare haren na zuwa ne bayan Janar Muhammadu Buhari da Goodluck Joanthan sun yi cacar baki game da matsalar tsaro a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.