Wasu Mutanen Damboa sun yi hadarin mota
Rahotanni daga Jihar Barno sun ce wasu 'yan gudun hijira daga Damboa da ke neman tsira da rayukansu sakamakon hare haren Boko Haram sun samu hadarin mota, inda yawancinsu suka jikkata. Kwamishinan yada labaran jihar Dr Muhammad Bulama ya tabbatar da faruwar hadarin
Wallafawa ranar:
Kwamishinan yace mutanen sun samu hadarin ne, a lokacin da suna gudun hijira akan hanyarsu zuwa Biu saboda halin kuncin da suka shiga a Damboa sakamakon munanan hare haren da Mayakan Boko Haram suka kai.
Mutane da dama ne dai aka ruwaito sun mutu a Damboa a jiya Juma’a bayan Mayakan Boko Haram sun bi gida gida suna jefa bama bamai tare da bude wa fararen hula wuta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu