Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun kasar Chadi sun ceto mutane daga hannun 'yan Boko Haram

Dakarun kasar Chadi sun yi nasarar ceto kimanin 85 daga cikin mutanen da ‘yan kungiyar Boko Haram suka sace, a arewa maso gabashin Nigeria. A karshen makon daya gabata ‘yan bindigan suka yi awon gaba da kusan mutane 100, da suka hada da mata, kuma suka kashe wasu 28, a wani samamen da suka kai a kauyen Doron Baga, dake kan iyakan Nigeria da kasar ta Chadi.Zuwa yanzu fiye da mutane 2,000 suka mutu cikin wannan shekarar, sakamakon tashe tashen hankulan da keda nasaba da kungiyar ta Boko Haran a Nigeria, yayin da wasu fiye da 650,000 suka rasa gidajensu. 

Mayankan kungiyar Boko Haram a Najeriya
Mayankan kungiyar Boko Haram a Najeriya AFP PHOTO / BOKO HARAM
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.