Isa ga babban shafi
Najeriya

Amnesty ta ce sojojin Najeriya sun yanka 'yan Boko Haram

A wani rahoto da ta fitar a wannan talata, kungiyar kare hakkokin bil’adama ta Amnesty International, ta zargi sojojin Najeriya da kuma ‘yan kato da gora da ke taimaka masu domin fada da Boko Haram, da cewa suna kashe jama’a ba tare da an tabbatar da sun aikata laifi ba ciki har da yanka makogoron mutane da wuka.

Sojojin Najeriya a Maiduguri
Sojojin Najeriya a Maiduguri REUTERS/Tim Cocks
Talla

Kungiyar ta ce tana da shaidu na faifan bidiyo da ke nuna yadda sojoji ke kama jama’a suna yankawa sannan suna jefa su a cikin manyan ramuka bisa zargin cewa ‘yan Boko Haram ne a cikin jihar Borno da ke arewa maso gabashin kasar.

Salil Shetty, babban sakataren kungiyar ta Amnesty, ya ce bai kamata gwamnatin Najeriya kasar da ya kamata ta kasance jagora a nahiyar Afirka ta yi wasa da wannan batu ba.

Har ila yau kungiyar ta nuna wani faifan bidiyo da ke nuna wani kauye da ‘yan Boko Haram suka kai wa hari tare da kashe mutane akalla 100.

Ma’aikatar tsaron Najeriya ta bayyana a wata sanarwa cewa, tana daukar wadannan bayanai na Amnesty da matukar muhimmanci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.