Isa ga babban shafi
Kamaru

Boko Haram: Kamaru ta tura Babban hafsan Sojanta zuwa arewaci

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya tura babban hafsan Sojan kasar zuwa yankin arewaci kan iyaka da Najeriya domin nazarin yadda dakarun kasar zasu yaki mayakan Boko Haram. Wannan kuma na zuwa ne bayan farmakin da mayakan suka kai a yankin, inda kashe mutane da dama tare da  sace Hakimin garin Kolafata da Uwar gidan wani kusan Gwamnati da kuma ‘Yan Sanda.

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Kamaru Paul Biya AFP PHOTO / REINNIER KAZE
Talla

Shugaba Biya ya shaidawa manema labarai cewa Kamaru zata sake aikawa da wasu karin dakaru zuwa yankin arewaci domin dakile ayyukan Mayakan Boko Haram da suka fara addabar yankin arewacin kasar.

A makon jiya ne dai gwamnarin Kamaru ta kori wasu Manyan Sojojin kasar bayan mayakan Boko Haram sun kashe akalla mutane 15 a arewacin kasar da ke kan iyaka da Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.