Isa ga babban shafi
Najeriya-Kamaru

‘Yan bindiga sun sace Uwargidan Mataimakin Firaministan Kamaru

Rahotanni daga Kamaru sun ce wasu ‘Yan bindiga da ake kyautata zaton Mayakan Kungiyar Boko Haram ne sun yi awon gaba da Uwar gidan Mataimakin Firamnistan kasar tare da wani Kaftin na Soja da ke tsaronsa a Kolafata a arewacin kasar, bayan Ministan ya zo bikin sallah a Marwa daga Yawundi.

Arewain garin Marwa a Jamhuriyar Kamaru
Arewain garin Marwa a Jamhuriyar Kamaru Getty Images/Anthony Ham
Talla

Garin Kolofata dai nan ne Mahaifar Mataimakin Firaminista Ahmadu Ali, kuma tana cikin karamar hukumar Mayo Sava da ke kan iyaka da Najeriya.

Rohotonni sun ce mutani shida suka rasa rayukansu a hare haren da ‘Yan bindigar suka kai.

Minister dai yazo da iyalan sa daga Yawunde don bukukuwan sallah, Amma ya tsira da ransa daga harin. Yanzu haka kuma wakilinmu Ahmed Abba yace Ministan yana garin Marwa Hedikwatar Arewa mai nisa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.